in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da babbar darektar kungiyar lafiya ta duniya WHO
2013-08-20 20:00:14 cri
Shugaban kasar Sin, Mista Xi Jinping, ya gana da Madam Chan Fung Fu-chun, babbar darektar kungiyar lafiya ta duniya WHO, a ranar Talata 20 ga wata, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A yayin ganawar, Mista Xi ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin ta tsaya kan manufar kula da rayuwar jama'a da kokarin amfanawa jama'a, inda ta dora muhimmanci sosai kan lafiyar jama'a. Don haka, gwamnatin za ta yi kokarin tinkarar duk wata matsala don zurfafa kwaskwarima kan tsarin aikin jinya, ta yadda za a samu damar warware wasu matsalolin da ke addabar jama'a, kamarsu kashe makuden kudade domin ganin likita, ko kuma wahalar ganin kwararren likita.

Mista Xi ya kara da cewa, kasar Sin na son kara hada kai tare da kungiyar WHO don yada fasahar jinya ta gargajiyar kasar Sin da magungunan gargajiyar kasar a kasashe daban daban, da kokarin taimakawa kasashen Afirka kafa wani tsarin aikin jinya da rigakafin cututtuka mai inganci, ta yadda za ta kara samar da gudummawa ga harkokin kiwon lafiya na duniya da tallafawa kokarin kasashen duniya na cimma muradun karni da MDD ta tsara.

A nata bangaren, Madam Chan ta yaba ma kasar Sin kan babban ci gaban da ta samu a kokarin daidaita tsarinta na fannin aikin jinya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China