Mai Magana da yawun shugaban kasar Mostafa Hegazi ya yi bayani dangane da kwabsawa da ake yi tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Morsi, ga manema labarai a birnin Alkahira ranar asabar inda yace Masar na fuskantar yaki ne da 'yan ta'adda.
Hegazi yaci gaba da cewa abin da yake faruwa a Masar da kuma zanga zanga da magoya bayan Morsi suke yi matakai ne na ta'addanci ba fafutuka irin ta siyasa ba.
Ya ce masu zanga zangar nuna goyon baya ga Morsi sun yi ta harbi da bindigogi inda suka hallaka mutane dake saman gidajensu , yayin da ya yi nuni da zanga zanga da akayi ranar juma'a 16 ga wata a kan wata gada, inda aka gano wasu masu zanga zanga dauke da makamai suna ta harbe harbe.
Hegazi ya kuma baiyana tsarin shugabancin Morsi tamkar mai tsattsauran ra'ayin addini ya kuma kira abubuwa da magoya bayan Morsi ke yi a matsayin ta'addanci. (Lami Mohammed)