Yin hadin gwiwa ta hanyoyi biyu zai inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata
A ranar 4 ga wata da yamma a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Li Keqiang da wakilan kasar Amurka da suka halarci shawarwari a tsakanin shugabannin 'yan kasuwa da masu masana'antu da tsofaffin manyan jami'an kasashen Sin da Amurka sun yi shawarwari kan batun raya dangantaka a tsakanin kasashen biyu da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu da dai sauransu. Li Keqiang ya bayyana cewa, yin hadin gwiwa ta hanyoyi biyu wato ta gwamnati da kuma jama'a zai inganta dangantakarsu yadda ya kamata.
Kamata ya yi bangarorin biyu su girmama juna kan manyan batutuwa da suke kulawa, da kara yin hadin gwiwar samun moriyar juna, da kuma hada kai a batutuwan duniya da yankuna, wannan zai taimaka wajen samun zaman lafiya da wadata a nahiyar Asiya da yankin tekun Pasific, har ma da dukkan duniya. (Zainab)