in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi shawarwari tare da sabon shugaban babban taron MDD karo na 68 Ashe
2013-08-14 20:58:02 cri
A ranar 14 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya yi shawarwari tare da sabon shugaban babban taron MDD karo na 68 Ashe da ke ziyara a kasar Sin.

Wang Yi ya bayyana cewa, babban taron MDD wani muhimmin dandali ne ga kasashe masu tasowa musamman ma kasashe matsakaita da kanana suke shiga harkokin kasa da kasa. Kasar Sin ta nuna goyon baya ga shugaban babban taron MDD da ya kara kyautata ayyukansu, kuma tana son maida batun samun bunkasuwar kasashe masu tasowa wadanda su ne yawancin membobin babban taron MDD a matsayin muhimmin aiki na MDD.

Ashe ya ce ya dora muhimmanci sosai kan muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a cikin harkokin kasa da kasa, kuma yana son kiyaye yin mu'amala da hadin gwiwa tare da kasar Sin kan ayyukan babban taron MDD a fannoni daban daban, kana za a ci gaba da samun goyon gaya daga kasar Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China