Kuma bisa labarin da shafin intanet mai kula da bala'in girgizar kasa ta Sin ya fidda, ran 22 ga wata, da karfe 7 da minti 45,ya nuna cewa, wata girgizar kasa mai karfin maki 6.6 ta abkawa yankin iyakar gundumar Min da gundumar Zhang, cibiyar girgizar kasa a arewacin layin da ya zagaye duniya na digiri 34.5 da kuma gabashin layin da ya keta duniya na digiri 104.2, kuma zurfinta ya kai kilomita 20.
Bala'in ya shafi garuruwa da dama da ke gundumonin biyu, inda layukan wayoyin sadarwa da kuma intanet na jama'a suka lalace, kana wutar lantarki ta dauke, ana kuma fama da bala'u da dama da suka hada da gangarowar duwatsu da laka da kuma zabtarewar kasa.
Kuma bisa labarin da rundunar 'yan sanda masu dauke da makamai ta samar, an ce, 'yan sanda guda 500 sun riga sun shiga wurare masu fama da bala'i, ciki har da masana masu ba da jiyya guda 120.
Kwamitin magance bala'un kasa, hukumar kula da tsaron lafiyar jama'a sun fara ayyukan samar da jinya ga bala'in da ya kai matsayi na hudu, kuma sun aika da wata kungiya zuwa wuraren don yin bincike kan yanayin wuraren da kuma ba da jagoranci. (Maryam)