Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mai da hankali sosai kan wannan batu, inda ya bukaci lardin Gansu da hukumomin da abin ya shafa da su kara kokarin yaki da bala'in girgizar kasa, tare da gudanar da aikin ceto yadda ya kamata, a kokarin rage yawan mutanen da za su mutu a sakamakon hakan.
Mr Xi Kuma ya bukaci a kara kulawa da mutane domin tsira daga bala'in da kuma tsugunar da su, da kara sa ido kan tartsatsin girgizar kasa, a kokarin daukar matakan yaki da sake abkuwar bala'in, da zummar rage hasarar da aka samu.
Firaministan Sin Li Keqiang shi ma ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da su dauki matakai nan take, tare da tura rukunonin aiki da kwararru zuwa yankuna da bala'in ya abkawa, a kokarin ba da jagoranci kan yaki da bala'in da gudanar da aikin ceto.(Fatima)