in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe manyan jami'an Boko Haram guda biyu a Nigeriya
2013-08-14 10:22:00 cri

A ranar Talata 13 ga wata, rundunar tsaro ta soja a Nigeriya ta tabbatar da cewa, ta harbe wassu manyan jami'an kungiyar Boko Haram su biyu a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin kasar a cikin wani hari da ta kaddamar wanda ya kunshi jami'an tsaro na musamman a garin Mubi.

Kwamandan sojan mai kula da tsare-tsare laftanar kanar Beyidi Martins ya sheda ma manema labarai cewa, shugabannin da aka tabbatar da kashe su a cikin wani samame da aka samu nasarar kai masu sun hada da Abubakar Zakaria da Mohammed Bama.

Ya yi bayanin cewa, an samu nasarar kai samamen ne sakamakon kokarin jami'an tsaron dake aiki a jihar, a cewarsa, an kame mutane 6 da ake zargi, sannan wassu guda 4 sun tsere da rauni a jiki. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China