Mahukuntar rundunar tsaron sojin kasar Nigeria sun musunta labaran da jaridar kasar Amurka, 'New York Times' ta buga cewar, sojoji na kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba a kokarin da ake yi na farautar 'yan ta'addan nan ta Boko Haram da suka yi sansani a jihohi uku da yanzu haka suke karkashin dokar ta baci.
Kakakin rundunar tsaron ta kasa Brig. Janar Chris Olukolade ya sanar da hakan jiya Asabar ga manema labarai, yana mai bayyana cewa, jaridar ta buga labaranta ne da niyyar saka wani yanayi a zukatan masu karanta jaridar, ta yadda za'a zata akwai tsananin hali na jin kai a yankin.
Olukolade ya ce, labarin ya ruwaito wassu mutane ba na gaskiya ba ne, ya kuma bayyana cewa, wai sojoji sun kasa tantance fararen hula da kuma 'yan ta'adda, suna mai cewa, sojojin sun juya bindigoginsu a kan fararen hulan da ya kamata su kare lafiyarsu.
Kakakin rundunar tsaron ya ce, wannan kwatancin da aka yi lallai ba na sojin Nigeriya ba ne, domin babu wanda ake kashewa babu gaira babu dalili kamar yadda jaridar ta 'New York Times' take iyakacin kokarinta na nunawa.
Idan ba'a manta ba, shugaban Nigeriya Goodluck Jonathan ya saka dokar ta baci a jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe, sakamakon tashin hankalin da 'yan ta'adda na Boko Haram suka jefa al'ummar wannan yanki a ciki. (Fatimah)