A jihar Bornon tarayyar Nigeriya, an sanar da cewa, yanzu haka yawan mutanen da suka mutu sakamakon wani sabon harin da aka kai a kauyen Konduga dake jihar Borno, a arewa masu gabashin kasar a ranar Talata, ya kai 50.
Kamar yadda basaraken kauyen Alhaji Zanna Musa Yale ya yi bayani ma gwamnar jihar Kashim Shettima lokacin da ya ziyarci kauyen domin jajanta musu tare da ganin iyakacin barnan da maharan suka yi.
Alhaji Zanna ya ce, yana kyautata zaton 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne suka yi wannan aiki da sanyin safiyar Lahadi lokacin da mazauna kauyen suka shiga masallaci sallan asuba.
Ya ce, maharan sun bi masallatai daya bayan daya da ake salla suka rika kashe mutane ta ko ina, wanda ya tabbatar da cewa, an kwashe gawawwaki 43 da hantsi, sannan sauran gawawwakin kuma an samo su a wani masallaci nan kusa. (Fatimah)