in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke wani shugaban kungiyar Boko Haram yayin sumame a Najeriya
2013-08-13 10:10:21 cri

An cafke wani shugaban kungiyar Boko Haram yayin sumame da jami'an tsaro suka kai a jihar Sokoto dake yankin arewa maso yammacin kasar Najeriya, makonni hudu bayan harbe daya daga cikin jigon kungiyar da ake nema ruwa a jallo, in ji sojin kasar ranar Litinin.

Mai magana da yawun sojin Musa Yahaya ya ce, wanda aka yi nasarar cafkewa sunansa Malam Mubarak, mai inkiya da 'dan hajiya, kana akwai wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne da aka cafke a lokacin sumamen da jami'an tsaron hadin gwiwa na soja da 'yan sanda suka kai a daren ranar Lahadi.

Ya ci gaba da baiyana cewa, cafke wanda ake zargin ya kuma kai ga sa'ar cafko wasu da ake zargi a kan hanyar Sokoto zuwa birnin Kebbi a ranar Litinin da safe, inda ya kara da cewa, yawan wadanda ake zargin da ake wa tambayoyi yanzu haka sun kai 20.

A ranar 11 ga wata, an kashe wani babban wanda ake zargi lokacin da jami'an tsaro suka yi musayar wuta da 'yan kungiyar Boko haram a maboyarsu dake unguwar Kalambaina-Gidan a cikin jihar.

A kuma ranar Asabar da ta wuce, sojoji sun kai sumame a wata maboyar 'yan tawayen a matsayin wani yunkurin kawar da 'yan kungiyar dake gujewa daga jihohin Borno, Yobe da Adamawa. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China