Sojojin Najeiiya sun bayyana ranar Litinin cewa, a kalla dalibai 7 da malamai 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Damaturu dake arewa maso gabashin Najeriya.
Masu tada kayar bayan sun kai harin ne da misalin karfe 9 da kwata na daren ranar Lahadi a makarantar sakandaren gwamnati (GSS) dake Damaturu, babban birnin jihar Yobe, wacce aka sawa dokar ta baci, in ji mai magana da yawun rundunar tsaron hadin gwiwa ta JTF Lieutenant Lazarus Eli.
Ya bayyana cewa, 'yan kungiyar ta Boko Haram sun bude wuta kan dalibai, inda 7 suka mutu nan take, kana 3 suka samu rauni, sa'annan suka nufi gidajen kwanan malamai, suka kashe guda 2.
Lt Eli ya ce, mayakan na Boko Haram sun yi kokarin kaiwa rundunar tsaro ta JTF hari a wajen bincike na kan hanya a babban birnin jihar, inda aka kashe uku daga cikinsu, kana sojoji uku suka samu rauni sakamakon musayar wuta.
Bugu da kari, dalibai 6 sun samu rauni, kuma an kai su asibiti suna karbar magani, in ji jami'in. (Lami)