in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mahara sun halaka mutane 35 a jihar Borno da ke Najeriya
2013-08-06 09:51:53 cri

Hukumomin soji a Najeriya sun bayyana a ranar Litinin cewa, wasu hare-haren da 'yan bindiga suka kai, sun yi sanadiyar mutuwar mutane 35 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wata sanarwa da kakakin rundunar tsaron hadin gwiwa da sojoji ke jagoranta(JTF) Laftana kanar Sagir Musa ya bayar wadda Xinhua ta samu kwafi, ta tabbatar da aukuwar hare-haren da ake zaton kungiyar Boko Haram ce ta kaddamar a ranar Lahadi.

Musa ya ce, 'yan bindigar sun kaddamar da wani mummunan hari kan ofishin 'yan sandan kwantar da tarzoma da ke garin Bama, wurin da a baya-bayan nan ya kasance inda 'ya'yan kungiyar ke kaddamar da hare-hare.

Kakakin sojojin ya ce, hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar 'dan sanda guda, 'yan kungiyar guda 17, kana wasu sojoji guda biyu sun jikkata.

Hari na biyu wanda sojoji biyu suka rasa rayukansu, an kaddamar da shi ne yayin da maharan suka yiwa wata cibiyar dakarun tsaron da ke yankin Malum Fatori a arewacin jihar dirar mikiya, cibiyar da ta kunshi dakaru daga Najeriya, Niger da kuma Chadi. Musa ya ce, yayin wannan harin, sojoji sun halaka 'yan kungiyar ta Boko Haram 15.

Kakakin sojojin ya ce, tuni dai aka killace yankunan, kuma al'amura sun dai-daita a garuruwan biyu da lamarin ya faru. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China