Kimanin mayakan kungiyar Boko Haram da ake tsare su a gidan yari na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar Najeriya sun bayyana cewa, a shirye suke na amincewa da tayin ahuwa na shugaba Goodluck Jonathan. Mayakan sun fadi cewa, a shirye suke na watsi da hare-haren da Boko Haram take kaiwa kasar da kuma amincewa da yin sulhu bisa matakin ahuwa na shugaban kasa. Daya daga cikin mutanen da ake tsare da su, Adam Konto, wani da ke cikinsu, ya sheda wa ministan harkokin na tsakanin gwamnati kuma shugaban kwamitin fadar shugaban kasa kan tattaunawa da warware kalubalolin tsaro ta hanyar sulhu a arewacin Najeriya, Kabir Taminu Turaki, a yayin ziyararsa a gidan yarin a ranar Talata cewa, dukkan wadanda ake tsare da su sun ce, a shirye suke ga barin daukar makamai kan kasa.
'Za mu daukar alkawari wajen taimakawa hukumomi idan suka ba mu sa'a ta biyu, da kuma amincewa da laifuffukan da muka aikata.' in ji Adam Konto. Haka kuma ya kara da cewa, 'Kungiya ta ja hankalinmu da wanke mana kai wajen gudanar da munanan ayyuka, gaskiya ba mu gane abin da muka aikata ba.'
A nasa bangare, malam Turaki ya yi alkawarin cewa, gwamnatin tarayya za ta duba wannan bukata tasu, idan har da gaske suke yi da bayanan da za mu samu daga wajensu masu amfani ne, domin sanya ku cikin wannan tsari na yin ahuwa.
A ranar 14 ga watan Mayu, shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya sanar da dokar ta bace a cikin Adamawa, Yobe da Borno dake arewacin kasar bayan yawan kasha-kashen mutane da hare-haren da ake dangantar su da kungiyar Boko Haram. Wadannan jihohi uku suna raba iyakoki tsakaninsu, sannan kuma suna raba iyakoki tare da kasashen Afrika uku wato Kamaru, Chadi da Nijar. (Maman Ada)