Rahotannin baya bayan nan daga Nijeriya na bayyana cewa, shugaba Goodluck Jonathan ya amince da dokar da ta haramta kungiyar nan ta Boko Haram a hukumce, tare da sanya ayyukanta a matsayin ayyukan ta'addanci.
Cikin wata sanarwa da ofishin kakakin fadar shugaban kasar Reuben Abati ya fitar, ta fayyace dokar da ta haramta wannan kungiya, kunshe da sashe na 5, daya cikin baka, wadda ya tanaji daurin a kalla shekaru 20 a gidan kaso, ga duk wanda ya taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda ta ko wace irin hanya.
Dokar, a cewar wannan sanarwa, ta shafi kungiyoyin Jamaatu Ahlis-Sunna Liddaawati Wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, da kuma Jama'atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan. Har ila yau, sanarwar ta ce, kafuwar wannan doka zai ba da damar hukunta laifukan da ke da alaka da wadannan kungiyoyi, karkashin tanade-tanaden dokokin hana ta'addanci na shekarar 2011. Wannan dai tanajin doka da ya haramta ayyukan kungiyoyin biyu, ya fayyace ma'anar taimakawa kungiyoyin, ciki hadda batun rufa ashirinsu, ko boye bayanai don gane da su, da kuma aiwatar da wata bukata domin amfaninsu.(Saminu)