in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tur da harin da aka kai a Nigeriya
2013-08-14 09:44:35 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon a Talatar nan ya yi suka da kakkausar murya a kan harin da aka kai a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeriya wanda ya hallaka mutane da dama.

Mr. Ban wanda yake ziyarar aiki a kasar Pakistan ya mika ta'aziyarsa ga iyalan mamatan, tare da yin kiran ga masu tsattsauran ra'ayin addini da su dakatar da harin da suke kaiwa, ya lura da cewa, babu wata bukatar da za'a iya cimma ta hanyar tashin hankali.

A cikin wata sanarwar da aka fitar daga ofishinsa, magatakardar ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su sulhunta kansu ta hanyar tattaunawa da sauran hanyoyin lafiya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China