in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun harbe mutane 15 a wani harin da aka kai ma wani kauye a Nijeriya
2013-06-07 10:10:11 cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samo mana labarin cewa, wassu 'yan bindiga da ba'a san ko su wane ne ba sun kai hari a unguwar Agatu dake kauyen Rukubi na yankin hukumar mulki na Ekye a jihar Nasarawa ta kasar Najeriya.

Babban jami'in 'yan sanda a jihar Umar Shehu wanda ya sanar da hakan ga manema labarai a Lafia, hedkwatar jihar, ya ce, an kai harin ne a wannan kauyen a ranar Talatar da ta gabata, amma har yanzu ba'a kama kowa ba, don haka ana nan ana cigaba da gudanar da bincike.

Wannan harin ya zo ne makonni kadan da harin da aka kai ma wassu jami'an tsaro inda aka hallaka 'yan sanda 49 da kuma jami'an liken asiri guda 10 a kauyen Alakyo, duk dai a jihar ta Nasarawa, harin da aka zargi kungiyar asirin nan ta Ombatse daga matsafan kabilar Eggon da aikata shi. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China