Wasu rahotanni daga majiyar kamfanin dillanci labarun kasar Sin Xinhua, sun tabbatar da hallaka a kalla mutane 60, sakamakon wasu hare-haren da wasu da ba'a tantance su ba, suka kai wasu kauyuka 4, dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, dake arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya.
Hare-haren na ranar Talata, a cewar majiyar Xinhua, sun ritsa ne da kauyukan Kizara, da Shemori, da Danjibga da kuma kauyen Keita. An kuma ce, maharan da yawansu ya kai kimanin mutane 100 dauke da bindigogi kirar AK47, da farko sun farma kauyen Kizara ne da misalin karfe 3 na dare, inda nan take suka hallaka mutane da dama, ciki hadda dagacin kauyen malam Bello Ibrahim.
Babban jami'in rundunar 'yan sandan jihar Usman Gwary ya tabbata da aukuwar wannan lamari, ko da yake dai bai yi wani karin haske don gane da batun ba. Shi ma wani jami'in tsaro da aka tura yankin da wannan balahira ta auku, ya bayyana wa Xinhua cewa, ko da yake ba a tabbatar da dalilin wadannan hare-hare ba, amma da ma a baya-bayan nan, akwai rahotanni kan yadda wasu bata-gari ke tare hanya, domin yi wa mata da kananan yara fashi, musamman ma a ranekun kasuwannin yankin.
Tuni dai jami'an tsaro suka fara gudanar da bincike kan wannan lamari, da nufin cafke wadanda ke da hannu cikin faruwarsa. (Saminu)