Mahukunta a jihar Yobe dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya sun ba da sanarwar rufe daukacin makarantun sakandaren dake jihar, bayowa bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kaiwa wata makaranta da asubahin ranar Asabar din da ta gabata, lamarin da nan take ya sabbaba rasuwar dalibai kimanin 20, baya ga wasu da yawa da suka jikkata.
Gwamnan jihar ta Yobe Ibrahim Gaidam ne ya ba da wannan sanarwa ranar Lahadi 7 ga wata. Sanarwar ta nuna cewa, 'yan makarantar za su koma karatu ne a zangon karatu na gaba dake tafe farkon watan Satumba mai zuwa. Da yake ba da wannan sanarwa, gwamna Gaidam ya bayyana goyon bayansa ga matakin kafa dokar ta baci da gwamnatin tarayya ta yi a jihar tasa, a hannu guda ya yi kira ga gwamnatin tarayyar da ta samar da tallafin sassauta halin da al'ummar jihar ke ciki sakamakon yanayin da ake ciki.
A wani ci gaban kuma shugaban majalissar dattijan Najeriya Sanata David Mark, da kakakin majalissar wakilai Aminu Waziri Tambuwal sun bayyana bakin ciki don gane da faruwar harin na jihar Yobe, cikin sanarwar da suka fitar jagororin majalissun dokokin biyu, sun yi Allah wadai da wannan hari, tare da kira ga rundunar jami'an tsaro da ta dauki matakan hana sake aukuwar lamari mai kama da wannan. Har ila yau, sun jajantawa iyalai da al'ummar jihar ta Yobe, don gane da aukuwar wannan hari. Sanata Mark da Tambuwal sun kuma jaddada aniyar majalissun biyu na goyon bayan duk wani yunkurin daidaita lamura a jihar ta Yobe, dama dukkanin fadin kasa baki daya. (Saminu)