in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jama'ar birnin Turpan sun yi Allah wadai da harin da aka kai wa gundumar Shanshan dake jihar Xinjiang
2013-06-30 20:51:34 cri
Zaunannen memban kwamitin birnin Turpan kuma mataimakin magajin birnin Lu Chunjing ya bayyana a ranar 30 ga wata a birnin cewa, harin da aka kai wa gundumar Shanshan a kwanakin baya ya kawo illa ga tattalin arziki da zamantakewar al'umma da rayuwar jama'a a birnin na Turpan, kuma daukacin jama'ar birnin da kabilu daban daban sun nuna takaici tare da yin Allah wadai da wannan hari.

Lu Chunjing ya bayyana cewa, gwamnatin birnin Turpan ta dauki matakai, da daidaita matsalolin da aka samu a sakamakon harin yayin da ake ci gaba da bunkasa tattalin arziki. Ya yi imani da cewa, a karkashin jagorancin kwamitin jam'iyyar kwaminis ta jihar Xinjiang mai zaman kanta, goyon baya da jama'a daga kabilu daban daban da kuma ayyukan hada kai a tsakanin kabilu, za a farfado da bunkasuwar tattalin arziki cikin hanzari, musamman ma sha'anin yawon shakatawa a birnin na Turpan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China