Rundunar sojin Najeriya ta bayyana gano gawar wani mutum, da ake zaton yana da alaka ta kud-da-kud da shugaban kungiyar maharan nan ta Boko Haram wato Abubakar Shekau.
Cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin daraktan watsa labaran ma'aikatar tsaron kasar, ta rawaito kakakin ma'aikatar Chris Olukolade na cewa, ana zaton mutumin ya rasu ne yayin da yake kokarin gabatar da wani aiki ga shugaban nasu, sai dai Olukolade bai bayyana sunan wannan mutum ba. Har ila yau sanarwar ta tabbatar da cafke karin wasu mutane biyu, ciki hadda 'dan Najeriya guda, yayin da suke kokarin tsallaka kan iyakar kasar da jamhuriyar Niger ta kogin Chadi, ana kuma tuhumarsu da hannu, cikin hare-haren da aka kai a garin Baga cikin watan da ya gabata.
Sanarwar ta kara da cewa, tuni aka kara yawan jami'an rundunar 'yan sandan kwantar da tarzoma a wasu karin garuruwa, domin aikin gudanar da tsaro da wanzar da zaman lafiya, duka dai a kokarin da ake yi na kakkabe 'yan ta'adda, da ayyukan ta'addanci daga dukkanin fadin kasar.(Saminu)