A yayin taron, mataimakin shugaban lardin Guangdong Lin Shaochun ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dukufa wajen ba da jinya ga mutanen da suka kamu da wannan cuta, da kuma amfani da dabarun zamani na kiyaye masu kamuwa da cutar, da samar da magunguna da kuma daukar nagartattun matakai domin ba da jiyya. Ya kuma jadadda cewa, a halin yanzu, ya kamata a mai da hankali kan rigakafin yaduwar cutar H7N9 ta hanyar yin bincike kan kasuwannin dabbobi da aka gano asalin wannan annoba ta yadda za' a iya kiyaye mutane masu kamuwa da cutar H7N9. Bugu da kari, ya kamata kungiyoyin kiwon lafiya su dukufa wajen yin bincike da kuma ba da jiyya ga mutanen da suka kamu da cutar. (Maryam)