in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya bukaci da a dauki kwararran matakai domin yaki da yaduwar cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9
2013-04-19 20:16:44 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga mahukuntan kasar da su dauki kwararran matakai, domin yaki da yaduwar cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9.

A cikin wata sanarwar da ofishin kwamitin tsakiya na JKS ya bayar a yau Jumma'a 18 ga wata, Shugaba Xi ya ce, ya kamata mahukuntan kasar su yi la'akari da tsaro da lafiyar jama'a, sannan su kara kokarin yin rigakafi da ba da jiyya ga wadanda suka kamu da wannan cuta.

Haka kuma, Shugaba Xi ya umurci da a bada jiyya ga wadanda suka kamu da cutar a yankunan dake fama da ita yadda ya kamata, da zummar rage yawan mutanen da za su rasu a sakamakon kamuwa da cutar bisa iyakacin kokari.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China