Hukumar kiwon lafiya da kayyade haifuwa ta kasar Sin ta ba da rahoto a daren ranar 18 ga wata cewa, daga karfe 5 na maraicen ran 17 zuwa karfe 5 na maraicen ranar 18 ga wata, an samu karin mutane biyar da aka tabbatar sun kamu da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9 a kasar Sin.
Ya zuwa yanzu, adadin mutane da suka kamu da wannan cuta a kasar Sin ya kai 87, daga cikinsu mutane shida sun samu lafiya, mutane 17 sun mutu, kuma sauran mutane 64 na cigaba da samun jiyya a asibitocin da abin ya shafa. Har ila yau, babu shaidu dake nuna cewa, wannan cuta na iyar yaduwa tsakanin Bil Adam. (Amina)