Hukumar kiwon lafiya da kayyade haifuwa ta kasar Sin ta ba da wata sanarwa a ran 21 ga wata cewa, ya zuwa karfe 4 na maraicen wannan rana, yawan mutane da aka tabbatar sun kamu da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9 a kasar Sin ya kai 102, daga cikinsu 20 sun mutu, 12 kuwa sun wartsake, sannan sauran 70 suna kwance a asibitocin dake wurare daban-daban.
Sanarwar ta ce, daga karfe hudu na yammacin ranar 20 zuwa karfe hudu da yammacin ranar 21 ga wata, an samu karin mutane 6 da suka kamu da wannan cuta a duk kasar. (Amina)