Yau Laraba 24 ga wata, mai ba da taimako ga babban jami'i mai kula da harkokin kiwon lafiya da muhalli na hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO Keiji Fukuda ya nuna cewa, matakan da Sin ta dauka domin kawar da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9 ya zama abin koyi ga duk duniya.
Daga ran 19 zuwa 23 ga wata, hadaddiyar kungiyar Sin da WHO ta duba aiki kan mutanen da suka harbu da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9 ta tantance halin da Sin ke ciki sakamakon barkewar wannan cuta, inda a ran 24 tawagar ta bada rahoto kan aikin, ta ce, ya zuwa yanzu, babu shaidu da ya nuna cewa wannan cuta zata iya yaduwa tsakanin mutum da mutum, amma har ila yau ba a tabbatar ko wannan cuta za ta iya yin haka ba tukuna, ya kamata Sin ta ci gaba da yin hadin gwiwa da bangarori daban-daban na cikin gida da kuma na kasa da kasa. (Amina)