An kara samun mutane 19 da suka kamu da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9 a kasar Sin a makon da ya gabata
Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya da kyayyade iyali ta kasar Sin ta bayar a ranar 1 ga watan Mayu, an ce, tun daga karfe 4 na yammacin ranar 24 ga watan Afrilu zuwa karfe 4 na yammacin ranar 1 ga watan Mayu, an samu sabbin mutane 19 da suka kamu da cutar murar tsuntsaye nau'in H7N9 a kasar. Ya zuwa yanzu, yawan mutane da suka kamu da cutar da aka samu a kasar Sin ya kai 127, a cikinsu guda 26 sun mutu, kana guda 26 sun samu lafiya.
A halin yanzu, mutanen da suka kamu da cutar na'u'in H7N9 sun zo ne daga birane 39 na larduna 10 na kasar Sin, kuma ba a gano alamar yaduwar cutar a tsakanin dan Adam ba. (Zainab)