in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar murar tsuntsaye H7N9 ta ci gaba da addabar kasar Sin
2013-04-27 13:59:27 cri

A ranar 26 ga wata, hukumar kiwon lafiya ta lardin Fujian dake kasar Sin ta tabbatar da samun dan gari na farko da ya kamu da cutar H7N9 a wurin, wanda ya cike yawan larduna da birane na kasar Sin da ake samu wannan cuta zuwa 9.

Ya zuwa yanzu, bisa rahoton da aka bayar, an tabbatar da mutane 118 da suka kamu da cutar murar tsuntsaye a kasar Sin, cikinsu mutane 24 sun rasu, sannan wasu 14 sun samu waraka.

Game da cutar, sassan na matakai daban daban sun inganta hadin gwiwa tsakaninsu don yaki da cutar. Ma'aikatar kula da jin dadin zaman rayuwar al'umma ta fidda manufa mai gatanci ga wadanda suka kamu da cutar wajen ganin likita da yin aikin jinya cikin sauki.

Ban da wannan kuma, a ranar 26 ga wata, hukumar da abin da ya shafa ta gwamnatin birnin Shanghai ta ba da labari cewa, rukunin bincike da yaki da cutar murar tsuntsaye H7N9 da ke kunshe da ma'aikatar kula da aikin gona ta Sin da hukumar kiwon lafiyar dabbobi ta duniya ya yi rangadin aiki ta kwanaki 2 a birnin Shanghai, kuma a cewarsa, matakan da aka dauka na gaggauta kafa tsarin yaki da cutar a birnin Shanghai, da rufe kasuwannin sayar da tsuntsaye na raye, sun samu sakamako mai gamsarwa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China