in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mandela ya 'dan samu lafiya
2013-06-28 10:24:12 cri

Fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta fada a ranar Alhamis cewa, tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela ya 'dan samu sauki, amma har yanzu yana cikin mawuyacin hali.

Kakakin shugaban kasar Afirka ta Kudu Mr. Jacon zuma, Mac Maharaj, ya ce, shugaba Zuma ya ziyarci Mandela a asibitin da yake kwance a Pretoria, inda likitoci suka shaida masa cewa, ya 'dan samu sauki, amma har yanzu dai yana cikin mawuyacin hali, dalilin da ya sa shugaba Zuma ya soke ziyarar da ya shirya kaiwa kasar Mozambique a ranar Alhamis

Shugaba Zuma ya ce, 'Wajibi ne mu yi wa Mandela addu'ar samun lafiya, kana mu ci gaba da gudanar da ayyuka da harkokinmu na yau da kullum, yayin da Mandela ke kwance a asibiti.'

Sai dai, an bayar da rahoton cewa, wani daga cikin iyalan Mandelan ya tabbatar da cewa, tsohon shugaban kasar ta Afirka ta Kudu, yana amfani da na'urar da ke taimakawa mutum yin numfashi, abin da ke kara nuna fargabar abin da ake ganin karshen fafutuwar da jagoran gwagwarmayar yaki da nuna wariyar launin fatan ke yi.

A ranar 8 ga watan Yuni ne aka kwantar da Mandela asibitin birnin Pretoria, kuma tun ranar Lahadi ne yanayin rashin lafiyar tasa ya tsananta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China