in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har yanzu Mandela na cikin mawuyacin hali
2013-06-27 10:10:29 cri

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Zacob Zuma, ya fada a ranar Laraba cewa, har yanzu tsohon shugaban kasar ta Afirka ta Kudu Nelson Mandela yana kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.

Shugaba Zuma ya fada a wajen taron kungiyar ma'aikatan ilimi na kasa, lafiya da sana'o'in hannu (Nehawu) a Boksburg da ke gabashin Johannesburg cewa, "Yayin da Mandela ke cikin mawuyacin hali, wajibi ne mu sanya shi tare da iyalansa cikin addu'o'i a kowa ne lokaci"

Wannan shi ne karo na hudu ke nan da shugaba Zuma yake bayyana cewa, tsohon shugaban kasar na cikin mawuyacin hali. Da farko ya bayar da sanarwa a ranar Lahadi da yamma cewa, rashin lafiyar Mandela ta tsananta, sannan a lokuta dabam-dabam ranar Litinin da Talata, ya ce, yanayin rashin lafiyar tasa bai canja ba.

Tun ranar 8 ga watan Yuni ne aka kwantar da Mandela a asibiti, sakamakon ciwon huhun da ya sake taso masa, Wannan shi ne karo na hudu da aka kwantar da Mandela a asibiti kuma mafi tsawo, tun a watan Disamban shekarar da ta gabata.

Duk da kyakkyawar kulawar da yake samu a asibitin kula da masu fama da ciwon zuciya da ke Pretoria, yanayin rashin lafiyar Mandela mai shekaru 94 sai kara tsananta take yi a 'yan kwanakin nan. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China