in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halin lafiyar Mandela ba shi da nasaba da ziyarar shugaba Obama, in ji shugaban Afirka ta Kudu
2013-06-25 10:14:38 cri

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya bayyana ranar Litini cewa, yanayin lafiyar tsohon shugaban kasar Nelson Mandela mai shekaru 94 wanda yanzu haka yake kwance a asibiti, na kara tsananta kuma ba zai shafi ziyarar da shugaban kasar Amurka Barack Obama zai kai kasar ba.

Zuma ya bayyana a birnin Johannesburg cewa, yanayin lafiyar Mandela ya kara tsananta a asibiti, to amman likitoci na bakin kokarinsu don sama masa lafiya da jin dadi.

An kwantar da Mandela a asibiti ran 8 ga watan Yuni saboda cutar huhu dake damun sa.

A ranar Lahadi da ta wuce, fadar shugaban kasar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, yanayin lafiyar Mandela na kara tsananta tun cikin sa'o'i 24 da suka wuce.

Zuma ya jadadda cewa, halin lafiyar ta Mr. Mandela ba zai shafi ziyara da shugaban kasar Amurka, Obama zai kai kasar Afirka ta Kudu ba.

Shugaba Obama zai kai ziyara a kasar Afirka ta Kudu ranar Juma'a mai zuwa a matsayin bangaren ziyarar aiki a kasashen Afirka guda uku.

Wannan shi ne karo na farko da shugaba Obama zai kai ziyara a kasar Afirka ta Kudu tun bayan hawansa kujerar mulki a shekarar 2009.

A ranar Juma'a da ta gabata ne mataimakin ministan dangantakar kasa da kasa da hadin gwiwa na kasar Afirka ta Kudu Ebrahim Ebrahim ya ce, ziyarar shugaba Obama za ta yi tasiri ga tattalin arzikin kasar Afirka ta Kudu. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China