in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron M.D.D ya zartas da wani kudurin da ke shafar batun Siriya
2013-05-16 09:14:20 cri

A ranar 15 ga wata, an yi babban taron M.D.D. karo na 67, inda aka zartas da wani kudurin da ke shafar batun kasar Siriya, kudurin da ya samu amincewa daga kasashe 107, da kuma rashin amincewa daga kasashe 12, a yayin kasashe 59 suke kaurace masa.

Kafin aka jefa kuri'a, zaunannen wakilin kasar Sin da ke M.D.D. Li Baodong ya bayyana cewa, yana fatan bangarorin daban daban za su mara wa sakataren janar na M.D.D. Ban ki-moon, gami da kasashen duniya baya, a wani kokarinsu na warware batun Siriya ta hanyar siyasa, kuma a cewarsa, tilasta zartas da kudurin a yayin da kasa da kasa ke fama da sabanin tsakaninsu, wannan ba zai yi amfani wajen ingiza kokarin warware batun ba. Haka kuma, Li Baodong ya ce, kullum kasar Sin ta kan nace ga bin hanyar warware batun Siriya ta hanyar siyasa. A yanzu haka, sakatare janar na M.D.D. Ban ki-moon da kasashen duniya suna wani sabon kokari na warware batun ta hanyar siyasa, sabo da haka, kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su amsa kiran da suka yi da nuna musu goyon baya, tare da bukatar gwamnatin Siriya da bangaren 'yan adawa na kasar da su dauki alhaki, su dakatar da tsagaita bude wuta nan take, da farfado da shawarwari na siyasa, da gaggauta lalubo bakin zaren warware wannan rikici.

A wannan rana, a hedkwatar M.D.D. dake birnin New York, sakatare janar na M.D.D. Ban ki-mooon ya yi shawarwari da firaministan kasar Birtaniya David Cameron, inda bangarorin biyu suka bayyana cewa, kamata ya yi a karfafa wa masu ruwa da tsaki na Siriya kwarin gwiwa  domin wannan na da muhimmanci gaske.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China