in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya bayyana jin dadinsa game da jinkirin da Sudan ta yi na rufe batutun man Sudan ta Kudu
2013-08-08 13:59:11 cri

Kakakin MDD Martin Nesirky ya bayyana a ranar Laraba cewa, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana farin cikinsa game da jinkirin da Sudan ta yi na rufe muhimmin layin bututun da ke kai mai zuwa Sudan ta Kudu ta yankunanta.

Ban Ki-moon ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa ta wayar tarho da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit a ranar Talata, inda ya ce, ya ji dadin shawarar da gwamnatin Sudan ta yanke ta dakatar da tura mai daga Sudan ta Kudu zuwa ranar 22 ga watan Agusta.

A ranar Litinin ne jaridar 'Almeghar Alsiyasi' da ke Khartoum ta ruwaito ministan man fetur na kasar Sudan yana cewa, an sanar da kamfanoni game da dakatar da rufe bututun da ke tura mai zuwa kasar Sudsan ta Kudu daga ranar 7 zuwa 22 ga watan Agusta.

Wannan sanarwa ta zo ne bayan ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Habasha Tedros Adhanom da kuma babban mai shiga tsakani game da batun Sudan da Sudan ta Kudu na kungiyar AU Thabo Mbeki suka kai Khartoum.

A baya dai gwamnatin Sudan ta tsai da ranar 7 ga watan Agusta, a matsayin ranar da za a dakatar da fitar da man Sudan ta Kudu zuwa ketare, inda ta zargi Juba da ci gaba da mara wa 'yan tawayen da ke yakar gwamnatin Sudan baya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China