A ranar Alhamis din nan kasar Sudan ta bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen Afirka, AU ta gabatar da wasu shawarwari don shawo kan matsalar mai da tashin hankali tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu.
Mai shiga tsakani na kungiyar AU Thabo Mbeki shi ne ya gabatar da shawarwarin ga gwamnatin kasar Sudan don a samu warware rikicin batun mai da kuma tashin hankali tsakaninta da Sudan ta Kudu, in ji cibiyar watsa labarum kasar Sudan (SMC)
Cibiyar watsa labaran ta SMC ta ba da rahoton cewa, mai magana da yawun ministan harkokin wajen kasar Sudan Abu Bakr Al-Siddiq na mai bayyana cewa, kasar Sudan za ta bayyana ra'ayinta bayan ta yi nazarin shawarwarin tare da karin cewa, Sudan ta tsai da matakin dakatar da fitar da mai daga kasar Sudan ta Kudu ne bayan dukkan kokarin da ta yi na ganin cewa, Juba ta aiwatar da yarjejeniya da aka kulla tsakanin kasashen biyu bai cimma nasara ba.
Al- Siddiq na fatan al'ummar duniya da sassa na shiyyoyi za su kara matsin lamba ta hanyar jan hankalin kasar Sudan ta Kudu da ta aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla da kuma nuna kokarinta a siyasance, inda ya kara da cewa, kasar Sudan ba ta da wata matsalar sake tattaunawa da Sudan ta Kudu idan ta nuna gaskiya kan yarjejeniyar.
A ranar Asabar da ta gabata, shugaba Omar Al-Bashir ya sanar da dakatar da fitar da man fetur na kasar Sudan ta Kudu ta cikin yankunan kasar Sudan daga ranar Lahadi.
A kuma ranar Laraba, ma'aikatar man fetur ta Sudan ta sanar da kamfanonin man fetur su daina fitar da man Sudan ta Kudu ta cikin yankunan kasar Sudan, in ji jaridar 'Alyaoum Altali' dake Khartoum. (Lami)