in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin man fetur na Sudan da Sudan ta Kudu sun tattauna yadda za'a fitar da mai
2013-05-24 10:14:41 cri

Ministan albarkatun man fetur na kasar Sudan Awad Ahmed Al-jaz da takwaransa na kasar Sudan ta Kudu Stephen Dhieu Dau sun tattauna a jiya Alhamis a birnin Khartoum, fadar gwamnatin kasar Sudan game da shirye-shiryen fitar da mai zuwa kasashen waje daga Sudan ta Kudu ta yankin kasar Sudan.

Ministocin biyu, a ganawar da suka yi da manema labarai bayan tattaunawar, sun jaddada muhimmancin dake akwai na gaggauta fitar da albarkatun man ta yankin kasar Sudan, inda ministan albarkatun man na Sudan Awad Al-jaz ya yi bayanin cewa, ana yin aikin jawo man daga rijiyar man na Fuluq zuwa ainihin wajen sarrafa shi a Al-jabalian dake cikin yankin Sudan, kuma yana samun cigaba a hankali.

Al-Jaz ya jaddada cewa, shirin aiwatar da hadin gwiwwa da kasashen biyu suka rattaba ma hannu a birnin Addis Ababa, kowanne zai tsaya a matsayin wani muhimman aiki da zai zama wani alheri ga cigaba da zumunci a tsakanin kasashen biyu.

Mr. Dau a nasa bangaren ya jaddada cewa, sarrafa man da fitar da shi waje ta yankin kasar Sudan zai inganta aminci tsakanin kasashen biyu tare da tabbatar da makoma mai haske.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China