in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta sanar da dakatar da jigilar man fetur din Sudan ta Kuda ta kasarta
2013-06-09 10:11:46 cri

Shugaban kasar Sudan Omar el-Bashir ya bayyana a ranar Asabar matakin dakatar da jigilar man fetur din kasar Sudan da Kudu ta hanyar bututun man dake ratsa kasarsa daga bakin ranar Lahadi.

'Mun baiwa Sudan ta Kudu lokacin daina baiwa 'yan tawaye tallafi, amma kuma ta cigaba da yin haka. Na umurci ministan man fetur da ya rufe bututun man dake ratsa kasar Sudan daga bakin ranar Lahadi.' in ji shugaba Bashir.

Shugaban kasar Sudan ya yi barazanar dakatar da jigilar man fetur din Sudan ta Kudu a cikin watan Mayu idan Juba ba ta daina taimakawa 'yan tawaye dake kai hare-hare kan rundunar sojojin Sudan a jihohin Kordofan da Blue Nile.

Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun samu matsaya guda a baya bayan nan wajen fara jigilar man fetur na Sudan ta Kudu ta hanyar bututun man dake ratsa kasar Sudan, bisa tsarin aiwatar da yarjejeniyar dangantaka da suka sanya hannu a Addis Abeba a shekarar da ta gabata a karkashin jagorancin kungiyar tarayyar kasashen nahiyar Afrika AU. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China