Yayin wani taron manema labaru da mataimakin kakakin MDD Eduardo del Beuy ya gabatar, ya bayyana ci gaba da kyautatuwar yanayi da ake samu tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, tare da fatan hakan zai bude sabon shafi ga huldar diplomasiyyar kasashen biyu.
Del Beuy ya ce, wata sanarwar da wakilin musamman na magatakardar MDD a Sudan ta Kudu Hilde Johnson ya fitar, ta nuna yadda lamura ke dada inganta tsakanin bangarorin da a baya suka sha fama da yanayi irin na zaman doya da manja, sai dai sanarwar ta ce, har yanzu, yankin Jonglei na kasar Sudan ta Kudu, na ci gaba da fuskantar yanayin zaman dar-dar.
Cikin sanarwar, Johnson ya bayyana farincinsa don gane da yadda kasashen makwaftan juna suka zartas da kudurin bude kan iyakokinsu, domin fara safarar danyan-mai cikin wannan mako.
A cikin watan Janairun bara ne dai kasar Sudan ta Kudu, ta dakatar da tura manta ta bututun dake Sudan, bayan da ta yi zargin cewa, Sudan din, na dibar wani kaso na man, a matsayin wani nau'in haraji. Daga baya kuma a ranar 8 ga watan Maris da ya gabata, kasashen biyu suka cimma yarjejeniya a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, don gane da batun zartas da shawarwarin da aka tsai da cikin watan Satumbar bara, shawarwarin da suka hada da batun mai do da aikin tura danyan mai ta bututun da suka ratsa kasar Sudan daga Sudan ta Kudu, cikin makwanni biyu da yanke shawarar.
Don gane da tashe-tashen hankula dake wakana a yankin Jonglei kuwa, sanarwar ta ce, kabilun Nuer da na Murley, dake matsayin manyan kabilun yankin ne ke fafatawa da juna, sakamakon rashin jituwa dake da alaka da mallakar wasu garken shanu.
Tuni dai kasar Sudan ta Kudu ta bayyana wannan yanki a matsayin wurin dake fama da annobar tashin hankali, ta kuma tura dakarun soji kimanin 3,000 domin dawo da yanayin zaman lafiya, baya ga wasu karin dakarun MDD 1000 da ke sintiri a yankin.(Saminu)