in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya yi barazanar dakatar da fitar da man fetur na Sudan ta Kudu
2013-05-28 10:08:53 cri

A ranar Litinin, shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir ya yi barazanar dakatar da fitar da man fetur daga kasar Sudan ta Kudu ta bututun Sudan, muddin kasar ta ci gaba da mara bayan 'yan tawayen 'Revolutionary Front' dake kudancin Kordofan.

A kwanan baya ne Khartoum da Juba suka kulla yarjejeniyar maido da fitar da man Sudan ta Kudu ta bututun kasar Sudan a matsayin matakin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, a shekarar da ta gabata.

Khartoum na zargin Juba da mara bayan 'yan tawayen 'Revolutionary Front' dake yakar gwamnatin Sudan a jihar kudancin Kordofan, to amma Juba ta musanta wannan zargi.

A ranar Litinin, dakarun kasar Sudan suka sanar da kwato garin Abu Kurshula dake kudancin Kordofan, daga wajen 'yan tawayen.

Mai magana da yawun dakarun gwamnatin Sudan Al-sawarmy Khalid Saad ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa, dakarun gwamnatin sun samu shiga garin Abu Kurshula, inda hakan ya sa sauran 'yan tawayen suka tsere daga yankin.

A halin da ake ciki kuma shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir a ranar Litinin ya ce, gwamnati ba za ta ci gaba da tattaunawa da 'yan tawayen 'Revolutionary Front' ba.

Ya ce, 'Daga yau, mun daina tattauanawa da masu cin amana, 'yan tawaye, 'yan yakin sa kai da ma dakarun Revolutionary Front', yayin da yake jawabi a wani taron jama'a a birnin Khartoum, bayan da sojojin gwamnati suka sanar da nasarar kwato garin Abu kurshula dake kudancin Kordofan daga wajen 'yan tawayen.

Zaman tattaunawa na baya bayan nan tsakanin gwamnatin kasar Sudan da 'yan tawayen SPLM na shiyyar arewa, karkashin jagorancin tawagar kungiyar tarayyar Afirka (AUHIP), a birnin Addis Ababa na kasar Habasha bai cimma nasara ba.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China