Ministan ma'aikatar man fetir na kasar Sudan Awad Ahmed Al-Jaz, ya umarci sashen ma'aikatarsa mai lura da sarrafa man fetir, da ya shirya karbar mai daga makwafciyar kasar, wato Sudan ta Kudu, ta bututu mallakar kasar ta Sudan.
Bisa shirin da aka yi dai, matatar man Sudan din dake jihar "White Nile", za ta fara amsar man da za a turo ne daga rijiyoyin hakar mai dake Malut a yankin Sudan ta Kudu, domin fidda shi zuwa ketare. Ministan wanda ya ba da wannan umarni ranar Talata 16 ga watan nan, ya kuma bayyana cewa, nan ba da jimawa ba, za a gudanar da bikin murnar sake ci gaba da fidda man kasar Sudan ta Kudu, ta tashoshin Al-Jabalain, da Higlieg, da kuma Port-Sudan, bisa sanya idon jami'ai daga bangaren kasashen biyu.
A halin yanzu dai, tuni wata tawagar jami'an ma'aikatar man ta Sudan, ta kai ziyarar gani da ido, domin tabbatar da yanayin da kayan aiki ke ciki a cibiyoyin sarrafa man kasar, duk dai a shirin da ake yi na karbar mai ta bututu, da ake sa ran fitar da shi zuwa ketare ta tashar ruwan Port-Sudan. (Saminu)