in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zartas da kuduri game da batun Siriya a M.D.D. ba zai yi wani amfani wajen warware batun ba, in ji kasar Sin
2013-05-16 16:56:40 cri

A ranar 15 ga wata da yamma, a gun taron M.D.D. ne, aka zartas da wani daftarin kuduri game da halin da ake ciki a Siriya da kasashen Faransa, Jamus, Birtaniya, Amurka da sauran kasashe 33 suka gabatar cikin hadin gwiwa. Game da halin da ake ciki a yayin taron.

A wannan rana, an shirya taron M.D.D. karo na 67 da ke da taken "Rigakafin rikici", inda aka zartas da wani sabon daftarin kuduri game da halin da ake ciki a kasar Siriya, da yawan kuri'un amincewa da suka kai 107, da kuri'un kin amincewa 12, da wasu kasashen da suke kauracewa wannan daftari. A cikin daftarin, an ce, ana dora muhimmanci sosai game da rikicin da ya ci gaba da tsananta a kasar Siriya, da yadda mahukuntan Siriya ke keta hakkin dan Adam, tare da yin barazana yin amfani da makamai masu guba. Kana daftarin ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su dakatar da tashe-tashen hankali, tare da sa kaimi ga kwamitin sulhu na M.D.D. da ya dauki matakai yadda ya kamata.

Shugaban taron M.D.D. karo na 67 Vuk Jeremic ne ya shugabanci taron kuma ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa,"A cikin kwanaki sama da 800 da suka gabata, rikicin ya ci gaba da tsananta a kasar Siriya, kuma ya lahanta mulkin kai da cikakken yanki na kasar, idan ba mu iya daukar wasu matakai don hana wannan masifa ba, ba za mu iya kare kwarjinmu a M.D.D ba, na yi imani cewa, yanzu, lokaci ya yi na kawo karshen wannan bala'i."

Vuk Jeremic ya jaddada cewa, kamata ya yi bangarorin da abin ya shafa su dauki matakai, don gaggauta farfado da shawarwarin siyasa game da batun Siriya, kuma muhimmin matakin da za a bi shi ne yarjejeniyar da rukunin game da batun Siriya ya cimma a gun taro na Geneva. ya ce,"Yau, dalilin da ya sa muka hallara a nan wato taron M.D.D. shi ne, domin nuna bayyana ra'ayoyinmu. Amma ya zama dole mu canja kokarin da muka yi zuwa hakikanin matakan da za mu dauka, kamata ya yi a dakatar da yin fito-na-fito kuma ba tare da gindaya wani sharadi ba a kasar Siriya, da sa kaimi ga bangarorin da rikicin Siriya ya shafa da su yi shawarwari, don samar da dauwamammen zaman lafiya a kasar. Haka kuma, ya zama wajibi kasashen duniya su martaba yarjejeniyar da rukuni game da batun Siriya ya cimma a watan Yuni na bara a birnin Geneva, da kuma yarjejeniyar da aka daddale a Moscow, don ci gaba da kokari, wajen gaggauta ingiza yunkurin siyasa a kasar."

A gun taron, zaunannen wakilin kasar Sin da ke M.D.D. ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta yarda da tilasta aikin jefa kuri'u kan daftarin kudurin, ganin irin sabanin da ke kasancewa tsakanin mambobin kasashe na majalisar, sabo da wannan ba zai taimaka wajen inganta hadin gwiwa tsakanin mambobin kasashen ba, kana ba zai kawo alfanu da kokarin da sakataren janar na M.D.D. Ban ki-moon da kasashen duniya suke yi wajen warware batun Siriya ba.

Li Baodong ya jaddada cewa, jama'ar kasar Siriya ne kadai za su iya zabar makomar kasar , a cewarsa, kasar Sin tana adawa ga yin shisshigin soji a kasar Siriya da ingiza canja mulki a kasar. Kamar yadda ya fada: "Kasar Sin tana tsayawa kan warware batun Syria ta hanyar siyasa. Yanzu haka, sakatare janar na M.D.D. Ban ki-moon da kasashen duniya suna kokarin shiga tsakani game da warware batun Siriya ta hanyar siyasa. Kasar Sin tana fatan bangarorin da abin ya shafa za su mara musu baya da amsa kirar da suka yi, gami da bukatar gwamnatin Siriya da bangaren 'yan adawa, da su dauki alhakin da ke wuyansu, don dakatar da tsagaita bude wuta nan take, da farfado da yin shawarwari na siyasa a tsakaninsu."

A wannan rana, kasashen Rasha, da Sin, da Koriya ta Arewa, da Iran, da Zimbabwe da sauran kasashe 7 sun jefa kuri'u na kin amincewa, yayin da kasashen India, Brazil, da Singapore, da Afrika ta kudu da ragowar sauran kasashe 55 suka kauracewa wannan kuduri, idan aka kwatanta yadda aka jefa kuri'un game da batun Siriya a M.D.D. a shekarar da ta gabata, an kara samun kasashen da suka kaurace kudurin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China