in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sa'o'i 72 suka rage wa 'yan takarar zaben shugaban Mali zagaye na biyu
2013-08-07 11:00:20 cri

Dan takarar jam'iyyar RPM, Ibrahim Boubacar Keita wato IBK wanda ya zo na farko da kashi 39.24 cikin 100 bisa yawan kuri'un da aka jefa, da Soumaila Cisse na jam'iyyar URD da ya zo na biyu da kashi 19.44 cikin 100 na yawan kuri'un da ya samu a zaben shugaban kasa zagaye na farko, kamar yadda lokaci ya nuna, sa'o'i 72 suka rage wa masu gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa domin janyo hankalin 'yan kasar Mali da su jefa masu kuri'a, wannan kuma dalilin rashin ba da sakamakon zabe na din din din daga babbar kotun kolin kasar.

Ministan hukumomin kasar Mali ya ba da sakamakon zabe na wucin gadi na zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Juli da ya kamata babbar kotun kolin kasar dake kunshe da mambobi tara ta amince, wanda ita ce hukumar kasa dake yanke shawarwari kan manyan batutuwan kasa, musamman ma da suka shafi zabubuka, kuma hukuncin da ta yanke ba ya ja da baya, a cewar dokar zabe. Sai dai a wasu rahotonnin da suke fitowa daga hedkwatocin wadannan jam'iyyun siyasa biyu, akwai yiyuwar kotun ta ba da ra'ayinta ranar yau Laraba. Idan haka ya kasance gaskiya, to wannan na nufin cewa, 'yan takarar na da kwanaki uku kadai da su gudanar da yakin neman zabe domin kira ga magoya bayansu da su jefa masu kuri'a. Kamar yadda dokar zabe ta kasar ta tanada, yakin neman zabe, ana kammala shi kwanaki biyu, kafin ranar zabe, wato ranar Jumma'a, ganin cewa, za'a shirya zabe zagaye na biyu a ranar Lahadi 11 ga watan Agusta bisa ga ajandar zaben da hukumomin kasar Mali suka gabatar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China