Dan takarar jam'iyyar RPM a zaben shugaban kasar Mali na shekarar 2013 Ibrahim Boubacar Keita da aka fi sani da IBK wanda ya zo na farko da kashi 39.24 cikin 100 na kuri'un zaben shugabn kasa zagaye na farko, ya yi kira ga magoya bayansa da su jefa masa kuri'unsu, ta yadda zai samu rinjaye da cimma nasara a lokacin wani taron gangami.
Bayan zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Juli, mista IBK ya bayyana a karon farko gaban jama'a a ranar Lahadi a cikin jawabinsa, dan takarar jam'iyyar RPM ya bukaci 'yan kasar Mali da suka zabe shi a zagayen farko da su kara ba da himma. Wadanda kuma ba su bukace su zabe shi ko kuma ba su je suka zabe ba, ina kira gare su da su ba da hadin kai ga jam'iyyar al'ammur kasa ta RPM domin 'dan takararta zai lashe zabe na nan gaba domin kasar Mali ta yi karfi cikin hadin kai da zaman lafiya, in ji mista IBK.
Tuni ma hedkwatar jam'iyyar RPM ta sanar da fara samun goyon bayan wasu 'yan takara. A cewar IBK, ranar 11 ga watan Agusta, ranar zaben shugaban kasa zagaye na biyu, wata hanya ce ta yin zabi tsakanin neman sauyi da tsarin da ya mai da kasa baya.
Abokin hamayyar IBK, a zagayen zaben shugaban kasa na biyu shi ne dan takarar jam'iyyar URD, mista Soumaila Cisse, wanda ya samu kashi 19.44 a zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Julin da ya gabata. (Maman Ada)