Wani gungun 'yan takara shida na zaben shugaban kasar Mali sun yi kiran magoya bayansu da su jefa ma Ibrahim Boubacar Keita da aka fi sani da IBK, dan takarar jam'iyyar RPM da ya wuce zagaye na biyu, bayan ya zo na farko a zaben ranar 28 ga watan Yuli da kashi 39.24 cikin 100 bisa yawan kuri'un da aka jefa a wani labarin da ya fito bayan wani taron manema labarai a birnin Bamako. Wannan kawance ya hada sabbin 'yan taraka na zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Yuli, kuma suka yanke shawarar ba da goyon bayansu ga Ibrahim Boubacar Keita. Wadannan manyan 'yan siyasa sun hada da Sibiry Coumare na jam'iyyar CIRA, Siaka Diarra na jam'iyyar UDF, Alhousseini Abba Maiga na jam'iyyar PANAFRIK, Moussa Mara na jam'iyyar YELEMA, Racine Seydou Thiam na jam'iyyar CAP da kuma Ousmane Ben Fana Traore na jam'iyyar PCR. Shugabannin jam'iyyun siyasa da suka ratttaba hannu, sun dauki niyyar kawo goyon bayansu da taimakawa shugaba Ibrahim Boubacar Keita a wa'adin mulkinsa wajen aiwatar da manufar tada komadar tattalin arzikin kasar Mali da kawo wadata ga 'yan kasa. A yayin da suke ba da dalilin wannan mataki nasu na hadewa da IBK, 'yan takarar shida sun bayyana cewa, sun dauki mataki ne domin maido da martabar Mali da maida wa 'yan Mali damar sake nuna kishi ga kasarsu tare da tashi tsaye wajen yaki da mulkin zalunci, tawaye, sumogal, ta'addanci, rashin adalci da cin hanci da rashawa, wadannan dalilai su ne hujjarmu na kawo goyon baya ga IBK. (Maman Ada)