Koda yake ance birbishin 'yan tawayen kasar dake Arewaci sun yi barazanar kaddamar da hare-hare a yankin. Ana dai sa ran lissafa kuri'un da ma'aikatan zabe suka yi hasashen zasu kai miliyan 6.87, da aka kada a runfuna 25,000 dake cikin kasar da kuma waje.
An dai jibge jami'an tsaro da dama a sassan kasar daban daban, domin tabbatar da doka da oda, yayin da kuma kimanin jami'an sa ido sama da 1,000, da suka kunshi na kungiyar ECOWAS da AU suka halarci sassan da ake gudanar da zaben.
Bisa tsarin zaben, idan har aka rasa daya daga cikin 'yan takarar 27 da ya samu kuri'u mafiya rinjaye, za a gudanar da zagaye na biyu a ranar 11 ga wata mai zuwa. Da yake bayyana ra'ayinsa jim kadan da kada tasa kuri'a, dan takarar jam'iyyar PRM, kuma tsohon firaministan kasar Ibrahim Boubacar Keita, ya ce zai karbi sakamakon zaben da za a fitar ba tare da wani ja-in-ja ba. Keita ya kuma bayyana kyakkyawan fatansa na lashe zaben, wanda ragowar manyan 'yan takara irinsu Soumaila Cisse na jam'iyyar URD, da Modibo Sidibe na FARE da kuma Dramane Dembele of the ADEMA ke fatan lashewa.
Rahotanni dai sun bayyana cewa Aichata Cisse Haidara ce mace daya tilo, da ta shiga domin a dama da ita a neman wannan mukami na shugabancin kasar ta Mali, ta kuma yi alkawarin inganta rayuwar mata da matasa, muddin al'ummar kasar suka bata wannan dama.(Saminu Alhassan Usman)