in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar binciken zargin amfani da makamai masu guba ta MDD na shirin tashi zuwa Syria
2013-08-07 10:37:17 cri

A ranar Talata ne MDD ta bayyana cewa, kwararrun da aka shirya za su binciki zargin amfani da makamai masu guba a kasar Syria, sun shirya don ziyartar kasar da ya ki ya wargaza.

Wata sanarwa da kakakin MDD Martin Nesirky ya raba wa taron manema labarai game da aikin tawagar MDD da za ta gudanar da binciken zargin amfani da makamai masu guba a kasar ta Syria, ta nuna cewa, shugaban tawagar farfesa Ake Sellstrom da 'yan tawagarsa sun hallara a birnin Hague, inda za su kammala kimtsawa kafin su tashi zuwa kasar ta Syria.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, hedkwatar MDD tana kokarin kammala matakan da suka dace bisa doka game da aikin binciken, kamar yadda aka cimma yarjejeniya da gwamnatin Syria a watan da ya gabata, kuma ana sa ran kammala wadannan shirye-shiryen cikin 'yan kwanaki.

Nesirky ya ce, an samu haske game da gudanar da binciken ne, sakamakon yarjejeniyar da aka cimma da gwamnatin Syria, yayin da babbar wakiliyar MDD game da shirin kwance damara Angela Kane da kuma sifeto Ake Sellstrom suka ziyarci Damascus.

An kafa tawagar bincike ta MDD ne a watan Maris bisa bukatar gwamnatin Syria, inda tawagar za ta binciki zargin amfani da makamai masu guba da aka ce an yi a garin Khan al-Asal da ke kudu maso yammacin wajen birnin Aleppo da kuma wasu wurare biyu a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China