Rundunar sojan kasar Syria ta tabbatar da cewa, dakaru 'yan adawa ta Free Syrian Army sun kashe fararen hula 7 da suka yi garkuwa da su a garin al-Khalidiya na birnin Homs.
A wannan rana kuma, gidan talabijin na Arabia wanda cibiyarsa ke birnin Dubai na Daular Tarayyar Larabawa ya ruwaito maganar dakaru 'yan adawa cewa, yayin da sojojin gwamnatin kasar ta yi musayar wuta da dakaru 'yan adawa, sun yi amfani da makamai masu nauyi da jiragen sama na yaki don harba boma-bomai a wuraren, inda suka haddasa mutuwa ko raunukar mutane masu dimbin yawa.
A ranar Talatar har ila yau, wani jami'i mai kula da harkokin kare hakkin dan Adam da na 'yan gudun hijira na MDD ya bayyana cewa, ba kawai matsalar Syria ta haddasa tabarbarewar yanayin kare hakkin dan Adam na kasar ba, hatta ma ta kawo wa duk yankin nan illa, ya kamata a warware matsalar a siyasance ba tare da bata lokaci ba.(Maryam)