Bisa labarin da aka samu ran 27 ga wata daga gidan talabijin na Al-Arabiya wanda hedkwatarsa ke birnin Dubai na Hadaddiyar daular Larabawa UAE. An ce kungiyar adawa ta nuna cewa, ran 26 ga wata da daddare, yayin da sojojin gwamnatin kasar ke kai farmaki a yankin Cubbon da ke birnin Damascus, sun yin amfani da iskar gas mai guba. Ta kuma bayyana cewa, sojojin gwamnatin ba kawai sun buga boma-bomai ne kan yankunan mazaunan wurin ba, sun kuma yi amfani da iskar gas mai guba, wadanda suka haddasa mutuwa da kuma raunatar da mutane.
Bugu da kari, bisa labarin da aka samu daga kamfanin dillancin labarai na kasar Syria, ran 27 ga wata, sojojin gwamnatin kasar Syria sun gano wata ma'aikatar da dakarun kungiyar adawa suke kera boma-bomai, inda suka samu na'urorin kera boma-bomai fiye da goma.
Ban da wannan kuma, an samu harin kunar bakin wake a wurin kusa da wani cocin dake kofar gabas ta tsohon garin Damascus ran 27 ga wata, wanda ya haddasa mutuwar a kalla mutane guda biyar, yayin da mutune takwas suka jikkata. (Maryam)