Shugaba Bashar al-Assad na Syria ya fada a ranar Lahadi cewa, kasarsa tana bukatar tattaunawar adalci tsakanin 'yan kasar, inda ya jaddada cewa, 'yan kasar ne kadai za su iya kawo karshen rikicin da aka shafe watanni 28 ana yi a kasar.
Shugaba Assad ya bayyana hakan ne yayin liyafar bude baki da aka gudanar a Damascus, babban birnin kasar wanda ya samu halartar kungiyoyin al'umma da wasu muhimman ministocin gwamnatinsa.
Shugaban ya jaddada bukatar tattaunawa a matsayin mafita ga rikicin da ake fama da shi a kasar, yana mai cewa, ba wanda zai iya warware ayyukan ta'addanci a Syria ta hanyar amfani da siyasa
Bugu da kari, Assad ya zargi kungiyoyin adawar Syria, musamman wadanda ke gudun hijira cewa, ba sa son warware matsalar kasar a siyasance domin a cewarsa, ba sa wakiltar kansa sai kasashen da ke ba su goyon baya. Ya kuma ce, gwamnatinsa a shirye take ta shiga tattaunawar zaman lafiyar da za a yi a Geneva, duk da cewa, bangaren 'yan adawar ba su da wakilci.
Don haka, ya ce, muddin ana bukatar a kawo karshen rikicin kasar, wajibi ne a yi amfani da duk wata hanyar da za ta taimaka wajen magance wannan matsala. (Ibrahim)