in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiyuwa ne za a yi babban taro game da kasar Sham a watan Yuli
2013-06-06 10:27:07 cri

Mai yiwuwa ne ba za'a iya shirya babban taro game da kasar Sham wanda ke da zummar duba yadda za'a warware rikicin kasar a siyasance ba a wannan watan na Yuni, kamar yadda aka shirya yi tun da farko, in ji kakakin MDD Martin Nesirky a lokacin ganawarsa da manema labarai.

Kakakin ya furta kalaman Lakhdar Brahimi, babban wakilin MDD da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa game da batun Sham wanda ya ce, har yanzu akwai ayyuka da yawa da ya kamata a yi kafin a shirya irin wannan babban taro, don haka ba za'a iya kiran taron a wannan watan ba.

Brahimi wanda shi ne tsohon ministan harkokin waje na kasar Aljeriya, ya sheda ma manema labarai a birnin Geneva sakamakon tattaunawar da aka yi a jiya Laraba tsakanin manyan jami'an kasashen Rasha, Amurka da kuma na MDD cewa, ya yi farin ciki game da yadda tattaunawar a wannan rana ta kasance cikin tsanaki kuma yana da tabbacin cewa, an dauki wassu matakai domin ganin an kira wannan babban taron a kan kasar Sham.

Brahimi ya yi alkawarin cigaba da tuntubar kasashen Rasha da Amurka game da shirya wannan babban taro a watan Yuli, yana mai bayanin cewa, za su sake ganawa a ranar 25 ga watan nan da muke ciki a Geneva, saboda halin da ake ciki a kasar Sham abin damuwa ne sosai. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China