Ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius ya bayyana a ranar Lahadi cewa, taron kasa da kasa kan batun samar da zaman lafiya a kasar Syria zai iyar gudana a cikin watan Yuli mai zuwa, tare da nuna cewa, wa'adin shirya wannan taro a cikin watan Yuni ya yi gajarta.
'Taron Geneve na biyu, a ganina shi ne taron karshe na cimma zaman lafiya. Ina fatan wannan taron zai gudana, kuma ina kyautata zaton cewa, za'a shirya shi a cikin watan Yuli.' in ji mista Fabius a cikin wata hirarsa da kafofin watsa labarai na Europe 1, I-Tele da Le Parisien.
Haka kuma mista Laurent Fabius ya kara da cewa, ya kamata 'yan adawar kasar Syria su zabi wakilansu, ko da yake wannan zai dauki lokaci, sannan kuma ya kamata a cimma matsaya guda kan jadawalin taro.
Jami'in diplomasiyar kasar Faransa ya bayyana damuwar kasar Faransa kan halartar Iran a wannan taro na Geneve.
Taron Geneve, zai taimaka wajen warware rikicin kasar Syria bisa kokarin da kasashen Amurka da Rasha suka yi na baya bayan nan, da zummar bude wani sabon babi bisa tushen shawarwarin siyasa. Hakazalika ya taimaka wajen sake kama bakin zauren taron da aka gudanar a cikin watan Yunin shekarar 2012 a Geneve, wanda shi ma manyan kasashen biyu suka yi tunanin shirya shi. (Maman Ada)