Gidan talabijin na al-Mayadeen da ke watsa shirye-shiryensa cikin harshen Larabci, ya bayyana cewa, sabon shugaban babbar kungiyar 'yan adawar Syria (SNC) da ke gudun hijira, ya yi tayin yin sulhu a ranar Lahadi a birnin Homs da ke tsakiyar lardin Syria a lokacin azumin watan Ramadan.
Yayin da yake kokarin sasantawa, Ahmed Jarba wanda aka zaba a matsayin shugaban SNC, sakamakon zaben da aka yi a Istanbul a ranar Asabar, ya kuma bayyana cewa, nan ba da dadewa ba, kungiyoyin adawar ke shirin samun makamai daga Saudiya.
Ko da yake, ana ganin da wuya wannan yarjejeniya ta cimma nasara, saboda galibin kungiyoyin 'yan adawar ba su bin umarni bai-daya saboda rashin shugabanci, an kuma gabatar da yarjejeniyar ce, lokacin da gwamnatin Bashar al-Assad na Syria ke ci gaba da samun nasara a yankuna da dama na kasar, galibi a yankin Homs.
An fara fadan na Syria ne tsakanin dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Syria da wadanda ke kokarin hambarar da ita tun ranar 15 ga watan Maris na shekara ta 2011, inda sama da mutane 90,000 suka halaka. (Ibrahim)